An tuhumi wanda ya sace matan nan uku a Amurka

Mutane uku da ake zargi da sace mata uku a jahar Ohio, Amurka
Image caption Mutane uku da ake zargi da sace mata uku a jahar Ohio, Amurka

'Yan sanda a jihar Ohio ta Amurka sun tuhumi wani mutum da laifin sace wa da tsare wa da kuma yiwa wasu mata uku fyade, a gidansa dake Cleveland.

'Yan sandan sun ce mutumin mai suna Ariel Castro yana basu hadin kai, inda yayi watsi da 'yancinsa na 'kin yin magana tare kuma da amincewa da a yi masa gwajin kwayoyin haihuwa.

Daya daga cikin matan uku dai ta haifi wata yarinya shekaru shida da suka gabata.

Wata majiya kusa da masu gudanar da binciken ta tabbatarwa da BBC cewa Amanda Berry da Gina DeJesus da kuma Michelle Knight an yi ta lalata dasu inda har a wasu lokuta sai da suka yi ta yin bari.

An kuma kame wasu 'yan uwan Ariel Castro su biyu wato Pedro da Onil, sai dai kawo yanzu ba'a tuhume su ba.

Mukaddashin kwamishinan 'yansanda Edward Tomba, babu wasu shaidu da suka nuna cewa suna da hannu a aikata laifin.