Jonathan ya yi taron gaggawa da jami'an tsaro

Goodluck Jonathan
Image caption Jonathan ya katse ziyarar da yake yi a Kudancin Afrika saboda matsalar da ake fama da ita

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya yi taron gaggawa da manyan jami'an tsaron kasar game da tashin hankalin da ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane a 'yan kwanakin nan.

Yawancin tashe-tashen hankulan dai na da alaka da addini.

"Taro ne na gaggawa da shugaban kasa ya jagoranta...saboda matsalar rashin tsaro da asarar rayuka," kamar yadda ministan kula da harkokin 'yan sanda Caleb Olubolade ya shaida wa 'yan jarida.

Na baya-bayan nan shi ne na ranar Talata, inda 'yan kungiyar matsafa ta Ombatse, suka yi wa jami'an 'yan sanda kwantan bauna a jihar Nasarawa, suka kashe 47 sannan suka kona gawarwakinsu.

Kuma har yanzu ba a ji duriyar wasu 'yan sandan 17 ba, a cewar rundunar 'yan sanda ta jihar.

Kwana daya kafin haka, an kashe mutane 55 a garin Bama na jihar Borno inda kungiyar Boko Haram ta kaddamar da hari a garin.

Jonathan ya katse ziyararsa

A wani harin mai alaka da addini, wasu 'yan bindiga sun kai hari a jihar Adamawa ranar Lahadi inda suka kashe mutane shida a wata kasuwa tare da harbe wasu hudu a wani coci.

Wannan ya faru ne kwanaki uku bayan an kashe mutane 39 a tashin hankali tsakanin matasan Musulmi da Kirista a garin Wukari na jihar Taraba.

A ranakun 16 da 17 ga watan Afrilu, mummunan tashin hankali tsakanin sojoji da masu tayar da kayar baya ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan 200 a garin Baga na jihar Borno.

Olubolade ya ce Jonathan ya kira taron ne tare da shugabannin sojojin kasa, na sama, da na ruwa domin lalubo hanyoyin shawo kan matsalar.

Sakamakon tashin hankalin, shugaba Jonathan ya katse ziyarar da yake yi a Kudancin Afrika "domin duba yadda matsalar take shi da kansa," a cewar sanarwar da ta fito daga ofishinsa.

A ranar Alhamis ya fasa kai ziyara kasar Namibia, inda aka shirya zai je bayan ziyarar da ya kai Afrika ta Kudu.

Ganin yadda hare-hare suka kazanta a tsakiya da kuma arewa maso gabashin kasar, Olubolade ya ce "abu mai muhimmanci shi ne a sake dabaru."

Karin bayani