An gano 'wurin sayar da yara' a Najeriya

Nigeria
Image caption Ana yawan samun safarar jarirai a Kudu masu Gabashin kasar a 'yan shekarun nan.

'Yan sanda a Najeriya sun ce sun gano 'yan mata 17 masu juna biyu a wani sumamaye da suka kai wani gida a jihar Imo da ke Kudancin kasar.

Sun ce suna kuma gudanar da bincike kan wata mace da suke zargin tana shirin sayar da jarirai.

Haka nan 'yan sandan sun ce sun samu yara kanana 11 da ake jiran masu bukatar sayensu su zo.

Ana yawan samun irin wannan aika-aika ta safarar jarirai a Kudu masu Gabashin kasar a 'yan shekarun nan.

Duk da cewa hukumomi na ikirarin cewa suna daukar matakai domin shawo kan matsalar.