Mutune 11 sun mutu a Karachi

Zaben kasar Pakistan
Image caption Zaben kasar Pakistan

A Pakistan ana can ana kada kuri'a a zaben kasa baki daya da ya yi fama da tashin hankali.

Hukumar zabe ta ce an sami fitowar jama'a sosai, kuma za a kara tsaawon sa'a guda na kada kuri'ar saboda dogayen layukan masu kada kuri'ar da ke akwai.

An sami wata fashewa a birnin Karaci, inda mutane goma sha daya suka mutu, arba'in kuma suka sami raunuka a gaban ofishin jam'iyyar Awami.

Jama'ar kasar dai suna fatar kyautatuwar al'amurra, kamar yadda wannan da mutumin da ya kada kuri'arsa ke cewa.