Mutane da dama sun mutu a Reyhanli

Harin bama bamai a Turkiyya
Image caption Harin bama bamai a Turkiyya

Hukumomin kasar Turkiya sun ce akalla mutane arba'in ne suka halaka a hare-haren bom na mota guda biyu, a kusa da kan iyakar kasar da Syria.

Mutane fiye da dari ne suka sami raunuka a fashewar a garin Reyhanli, inda ke da 'yan gudun hijirar yakin da ake yi a Syria.

Wani da ya ga abin da ya faru ya ce "Bom din ya fashe ne ba zato ba tsammani. Ina tsaye ne a can sai kawai bam din ya tashi."

Mataimakin Firaministan Turkiiya ya ce sojin leken asiri na Syria ne ake zargi da kai harin.