Akalla mutane 18 ne suka mutu a Turkiyya

Hukumomin Turkiya sun ce akalla mutane goma sha takwas ne suka mutu a harin bom a mota, a wani gari da ke kan iyaka da Syria.

Shedu a Reyhanli, kilomita kadandaga muhimmin mashigi na kan iyaka, sun ce akalla fashe-fashe hudu ne suka auku a tsakiyar garin.

Garin Reyhanli yana da sansanin 'yan gudun hijira na rikicin da ake yi a Syria.

Da yake magana da BBC daga Sansanin 'Yan Gudun Hijira na Zaatari a Jordan, Kwamishinan Agajin Jin Kai ta Tarayyar Turai, Krisatalina Gergieva, ta ce lalle a kara yin hubbasa wajen agajin wadanda suka tashin hankalin ya shafa.