Akwai sabon nau'in cutar nimoniya! Inji WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce ana ta kara ganin alamar cewa wani sabon nau'in cutar corona ko kuma kambi, mai wanzar da ciwon hakarkari na limoniya, za a iya dauka daga wani mutum zuwa wani.

A Faransa ma mutum na biyu yana can rai kwakwai-mutu kwakwai, bayan da ya kwanta daki da wani mai fama da cutar.

Sai dai ministar lafiyar Faransar, Marisol Tourain, ta ce bai kamata jama'a su damu ba.

Tun daga bara zuwa bana, mutane talatin da hudu ne aka san cutar ta kama, inda galibin wadanda suka rasu a kasar Sa'udiya ne