Jama'a na bukatar 'agajin abinci a Nijar'

Jama'a na bukatar 'agajin abinci a Nijar'
Image caption Fari na daga cikin abinda ke haifar da matsalar

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane 800,000 ne ke fuskantar karancin abinci a jamhuriyar Nijar kuma kimanin 84,000 daga cikinsu na bukatar agajin gaggawa a daidai lokacin da matsalar abinci ke kara kamari a kasar.

Matsalar fari da mutuwar amfanin gona, na daga cikin dalilan da ofishin kula da agaji na Majalisar Dinkin Duniya ya bayar, wurin gargadin cewa ana fuskantar babbar barazanar yunwa daga watan Juni zuwa Agusta.

Sanarwar da ofishin ya fitar ta ce daga cikin mutane 800,000 din da ke bukatar agajin abinci, 84,000 ba su ajiye komai ba, kuma suna bukatar agajin gaggawa.

Kasar ta Nijar dai ta sha fama da matsalar karancin abinci a baya sakamakon rashin kyawun damina da kuma fari - abinda a wasu lokutan ke kaiwa ga mutuwar mutane musamman yara kanana.

A shekara ta 2011 ma...

Majalisar ta ce lamarin ya fi kazanta ne a yankunan Tillaberi da Tahoua, da kuma kudancin Zindar.

Kwararowar 'yan gudun hijira daga kasar Mali - inda ake gwabza yaki tun farkon bana - ya kara kazanta halin da ake ciki a Tillabery da Tahoua.

Ta kara da cewa tuni matsalar ta fara sanya wasu mutane sayar da dabbobinsu ko kuma kayan noma domin samun na kalaci.

A shekara ta 2011, kimanin mutane miliyan shida matsalar ta shafa - bayan da fari ya ci karo da 'yan ciranin da suka koma gida daga kasashen Libya da Ivory Coast inda aka yi fama da yaki.

MDD ta ce Kasar ta nemi agajin dala miliyan 354 a watan Fabreru domin tunkarar matsalar ta bana - sai dai kashi biyu bisa uku kawai na kudin aka samu.

Karin bayani