Firaministan Turkiya ya ce wasu suna son jefa kasar yin yaki da Syria

Racep Tayyip Erdogan
Image caption "Za mu yi aiki da hankali"

Firaministan Turkiya, Racep Tayyip Erdogan, ya ce munanan hare-haren bamabamai a mota guda biyu, da aka yi a garin Reyhanli na kan iyaka a Turkiyar jiya Asabar, nufinsa shi ne a ingiza kasar ta yi yaki da Syria.

Ya shaida wa magoya bayansa cewa lalle ne Turkiyar ta yi aiki da hankali a lokacin da ake takalarta.

Mutane arba’in ne suka rasa rayukansu a wadannan hare-hare, yayin da fiye da mutane dari suka sami raunuka.

Syria dai ta musanta alhakin kai hare-haren.

Ministan watsa labarai, Imran al Zoubi, kusan a Turkiyar ce ke da alhakin haka bisa jawo ma kanta da ta yi.

Ya ce, "Mu abin da muke cewa shi ne, duk wani abu da ya auku a Syria alhakin gwamnatin Turkiya ne da sauran ire-irenta, shakka babu."