'Boko Haram ce ta kai harin Baga da Bama'

Image caption Boko Haram ta yi ikirarin kai hari Baga da Bama

Kungiyar Jama'atu ahlulsunna lil da'awati wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram sun yi ikirarin cewa su ne suka kai harin garuruwan Baga da kuma Bama duk a Jihar Borno.

Shugaban Kungiyar Imam Shekau ya yi wannan kalaman ne a wani faifan video wanda suka fitar.

Kungiyar ta ce ta kama wasu mata da kananan yara don mayar da martani ga kama nasu iyalan da suke zargin Jami'an tsaro ke yi.

Shugaban Kungiyar ahlusunnah lildawati wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram Imam Abubakar Shekau ya bayyana ne da kayan soji a jikinsa rike da takartar da yake bayani da bindiga a gefensa.

Sai dai Shugaban Kungiyar ya zargi Jami'an tsaro da kashe mutane da kuma kona gidaje a Baga, ya kuma musanta ikirarin Jami'an tsaron Najeriya cewa sun kashe yan Kungiyar talatin.

Haka kuma a jawabin nasa na tsawon mintina 12 Imam Shekau ya ce sun kama mata da kananan yara saboda kama musu nasu matan da yara.

Idan dai kama matan da yaran ya tabbata shi ne karo na farko da suka kama mata da kananan yara 'yan Najeriya don neman biyan wasu bukatun su inda suke cewa ba za su saki wadanda suka kaman ba sai an saki matayensu da kuma 'ya'yansu da aka kama.

Haka kuma ya kara da cewa, ba za su bar aiyukan da suke yi ba kuma ba wani batun sulhu tsakaninsu da gwamnati.

Gwamnatin Tarayya dai ta kafa kwamitin yin afuwa ga yan Kungiyar da zummar kawo karshen tashe tashen hankula a kasar.

Shugaban ya yi gargadi ga yan jaridu cewa babu wanda yake wakiltar su sai wani da ake kira Abu Zinnira saboda haka su guji ganawa da wasu da suke ikirarin suna wakiltar 'yan kungiyar.

Haka kuma a cewar shugaban za su dauki mataki kan wadanda suke yi musu makarkashiya.

Karin bayani