Safarar makamai: An yankewa ɗan Iran hukunci

Image caption Lokacin da aka kama makaman a Lagos

Wata kotun birnin Lagos ta yankewa wani ɗan ƙasar Iran, Azim Aghajani da abokin hulɗarsa ɗan Najeriya, Ali Abbas Jega hukunci dangane da safarar makamai ta tashar jiragen ruwa ta Lagos.

An yankewa mutanen biyu hukuncin zaman gidan kaso na shekaru biyar.

An dai kama mutanen biyu ne a shekara ta 2010 yayin da suke kokarin kai wasu makamai da aka ce, anyi nufin kai su kasar Gambia ne.

Sai dai kuma lauyoyin mutanen biyu sun ce, zasu ɗaukaka ƙara.