Benue: An kashe mutane 57

Rahotanni daga jihar Binuwai dake tsakiyar arewacin Nijeriya na cewa mutane kimanin hamsin da bakwai ne suka rasa rayukansu kana aka ƙona ƙauyuka da dama.

Lamarin dai ya auku ne sakamakon a wani tashin hankali tsakanin 'yan ƙabilar Agatu da kuma Fulani makiyaya.

Haka nan kuma an kashe shanu masu yawan gaske a lamarin.

Ɓangarorin biyu dai na zargin juna da tayar da rigimar a ƙaramar hukumar Agatu.

A jihar Binuwai da ta jima fama da rikici tsakanin Fulani makiyaya da kuma manoma.