'Tsani muke nema zuwa Imam Shekau'

Image caption Wadansu daga cikin 'yan kungiyar 'Boko Haram'

Kwamitin da gwamnatin Najeriya ta kafa don ya duba hanyoyin yi wa 'yan kungiyar Jama'atu Ahlis Sunnah lid Da'awati wal Jihad—wacce aka fi sani da suna Boko Haram—afuwa ya mayar da martani dangane da faifan bidiyon da kungiyar ta fitar wanda a ciki ta yi ikirarin cewa ita ce ke da alhakin kai hari a garuruwan Baga da Bama na Jihar Borno.

Shugaban kwamitin, kuma ministan ayyuka na musamman, Alhaji Tanimu Turaki, ya shaida wa BBC cewa abin da kwamitin ke so ya yi shi ne fito da wani tsari da za a yi sulhu.

A cewarsa, "Imam [Abubakar Shekau] yana cewa su za su bi sunnar Manzon Allah (SallalLahu Alaihi wa Sallama)—wannan abin jin dadi ne a gu na, domin Manzon Allah (SallalLahu Alaihi wa Sallam) ya zauna ya yi sulhu; mun san sulhun da aka yi na Hudaibiyya.

"Idan aka ce za a yi sulhu—eh, an san kowa ba zai samu abin da yake so ba amma—abu mafi muhimanci shi ne a zauna, a sasanta, a tattauna".

Ya kuma kara da cewa "Ni a fahimta ta, ba wai [Imam Shekau] ya ce ba zai yi sulhu ba ne; abin da yake cewa idan za a yi sulhu, a tsaya a bi ta hanya wadda ta dace, a yi da mutanen da ya kamata a yi sulhu da su. Kuma mu kokarin da muke yi, ai muna neman tsani ne da zai kai mu wurinsa domin a tsaya a tattauna, a yi magana tsakani da Allah".

A faifan bidiyon dai kungiyar ta kuma yi ikirarin cewa ta kama wadansu mata da kananan yara don mayar da martani ga kame na su iyalan da suke zargin jami'an tsaro suna yi.

Karin bayani