Shugaba Jonathan ya kafa dokar ta-baci

Goodluck Jonathan
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya ayyana dokar ta-baci a jihohin Adamawa, da Borno, da Yobe.

Yayin wani jawabi da ya yi ta kafofin yada labarai na kasar, Shugaba Jonthan ya ce yin hakan ya zama wajibi ne saboda "yaduwar ayyukan 'yan ta'adda, da kuma kalubalen tsaro da ya ki ci ya ki cinyewa a wadansu sassan kasar, musamman ma a [jihohin] Borno, da Yobe, da Adamawa, da Gombe, da Bauchi, da Kano, da Filato, da kuma na baya-bayan nan, Bayelsa, da Taraba, da Benue, da Nasarawa".