Najeriya: Shugaba Jonathan ya kafa dokar ta-baci

Goodluck Jonathan
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya ayyana dokar ta-baci a jihohin Adamawa, da Borno, da Yobe.

Yayin wani jawabi da ya yi ta kafofin yada labarai na kasar, shugaban na Najeriya ya ce, "Sakamakon abubuwan da suka faru kwanan nan a jihohin da abin ya shafa, ya zama wajibi gwamnati ta dauki wani muhimmin mataki don maido da zaman lafiya.

"Kuma bayan tuntubar juna, zan yi amfani da damar da Sashe na 305, karamin sashe na 1 na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 wanda aka yiwa gyara ya ba ni, in ayyana Dokar ta-Baci a jihohin Borno, da Yobe, da Adamawa".

Ya kuma ce a dalilin hakan tuni aka umarci babban hafsan tsaro na kasar ya aike da karin sojoji wadannan jihohi ba tare da bata lokaci ba don su tabbatar da tsaro.

Amma kuma, a cewar Mista Jonathan, gwamnoni da sauran masu rike da mukaman siyasa a jihohin za su ci gaba da rike mukamansu.

Shugaba Jonthan ya ce jawabin nasa ya zama wajibi ne saboda "yaduwar ayyukan 'yan ta'adda, da kuma kalubalen tsaro da ya ki ci ya ki cinyewa a wadansu sassan kasar, musamman ma a [jihohin] Borno, da Yobe, da Adamawa, da Gombe, da Bauchi, da Kano, da Filato, da kuma na baya-bayan nan, Bayelsa, da Taraba, da Benue, da Nasarawa".

Sai dai kuma ya jaddada cewa ko da yake za a ci gaba da yunkurin tattaunawa da sasantawa, gwamnati na da alhakin tabbatar da tsaron jama'a da kuma kare martabar Najeriya; don haka ba za ta taba yin shakkar daukar duk matakin da ya wajaba don tabbatar da hakan ba.

Shugaban na Najeriya, wanda kuma ya yi Allah-wadai da kisan jami'an tsaron da aka yi kwanan nan a Jihar Nasarawa, ya kara da cewa: "Ayyukan wadannan 'yan ta'adda abin Allah-wadai ne da ke haddasa fargaba a tsakanin al'umma da kuma kusan durkushewar doka da oda a wadansu sassan kasar, musamman a arewa".

Mista Jonathan ya kuma ce gwamnatinsa ta dauki matakan magance matsalolin da suka haifar da wadannan rikice-rikice, amma ga alama "masu tayar da kayar baya da 'yan ta'adda na wani shiryayyen yunkuri na daidaita kasar ta Najeriya".

Daga nan ya ce bayanan tsaron da ya samu sun nuna cewa wadannan matsaloli na tsaro tawaye ne ga hukumomin kasar daga masu tayar da kayar baya da 'yan ta'adda wadanda ke barazana ga hadin kan kasa.

"Tuni ma", in ji Mista Jonathan, "wadansu kungiyoyi wadanda ke mubaya'a ga akidun da suka [saba da na Najeriya] su ka mamaye arewacin Jihar Borno.

"Ga alama wadannan kungiyoyi sun jajirce sai sun girka iko da mulkinsu a wannan sashe na kasarmu abar kaunarmu; daga can kuma, sannu a hankali, su mamaye sauran sassan kasar".

A cewar shugaban na Najeriya, ayyukan wadannan kungiyoyi ayyana yaki ne da kuma zagon kasa ga halalcin hukumomin Najeriya, sannan ya ce: "A matsayinmu na gwamnatin da ta san ciwon kanta, ba za mu nade hannu muna kallo haka na faruwa ba".

Daga nan Shugaba Jonathan ya ce a baya gwamnatinsa ta dauki matakan kawo karshen wannan al'amari ta hanyar rarrashi da tattaunawa da kuma tuntubar juna da shugabannin siyasa, da na addini, da na al'umma a jihohin da abin ya shafa.

Ya kuma ce za a mika cikakken bayanin wannan mataki da gwamnati ta dauka ga Majalisar Dokoki ta kasa kamar yadda Kundin Tsarin Mulki ya tanada.