An soma tura jami'an tsaro a wasu jihohin arewa

sojoji
Image caption Wasu sojoji a Maiduguri

A Najeriya , yanzu haka an soma tura karin jami'an tsaro zuwa jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa da Shugaban kasar, Goodluck Jonathan ya kafa dokar ta baci a cikinsu,a wani yunkurin tabbatar da tsaro a cikinsu.

Rundunar tsaron kasar cikin wata sanarwa da kakakinta Birgediya Chris Olukolade ya aikewa kafafen yadda labarai ta ce tuni aka tura karin sojoji da 'yan sanda zuwa yankunan da dokar za ta yi aiki domin kawo karshen zubar da jini.

A Jihar Adamawa koda yake rahotanni sun ce an tura karin sojoji a jihar bayan shelar, babu wata alamar da ta nuna cewa an baza su a kan titunan Yola, fadar gwamnatin jihar.

Karin bayani