An kashe Fulani a jahar Tilaberi

A jamhuriyar Nijar, wata arangama da aka yi tsakanin dakarun yan tawayen MNLA na Mali da wasu makiyayan Nijar na arewacin jahar Tillaberi ta yi sanadiyar mutuwar yan tawayen MNLA biyu yayin da su kuma suka yi awon gaba da bafillatani daya.

Hakan ya faru ne kusa da iyaka tsakanin kasar ta Nijar da makwabciyarta Mali, kuma tuni hukumomin na Nijar suka tura sojoji zuwa yankin domin sa ido a kan duk wasu abubuwan da ka iya faruwa.

Yanayin tsaro dai a arewacin Nijar ya ci gaba da tabarbarewa ne tun bayan da dakarun Faransa tare da hadin guiwar dakarun warzar da zaman lafiya na ECOWAS suka fatattaki 'yan tawaye da masu kaifin kishin Islama daga arewacin Mali.