Syria ta yi amfani da makamai masu guba! Obama

Ana zargin Syria da amfani da makamai masu guba
Image caption Ana zargin Syria da amfani da makamai masu guba

Shugaban Amirka Barack Obama yace ya ga hujjojin da suka nuna ana amfani da makamai masu guba a Siriya.

Sai dai yace yana da muhimmanci a sami kwararan bayanai game da abin da ya faru.

Shugaban na Amirka yace ana nazarin dukkan matakai da suka hada dana diplomasiyya da kuma matakan soji, yana mai cewa dubban jama'ar da suka rasu a Siriya a sakamakon amfani da muggan makamai sun isa hujjar da ya kamata gamaiyar kasa da kasa su dauki mataki.

Mr Obama na magana ne bayan ganawa da Firaministan Turkiya Racep Tayyip Erdowan a fadar white house.

Karin bayani