An samu shedu game da kai hari da makamai masu guba a Syria

Wani dan Syria
Image caption Wani dake ikirarin ya shafu da makami mai guba a Syria

BBC ta samu bayanai daga wasu shaidu da suke tabbatar da rahotannin da suka ce, an kai hari da makamai masu guba a wani gari dake Syria cikin watan jiya.

Wasu sun fadawa wakilin BBC da ya ziyarci garin Saraqeb dake kudu maso yammacin birnin Aleppo cewa, jirage masu saukar unugulu na gwamnati sun jefa wasu abubuwa biyu dake dauke da guba.

Kuma wani likita da ya duba wata mata da ta mutu yace, ya ga alamun gubar a jikinta.

Gwamnatin Syria da kuma 'yan tawaye dukka sun sha musanta cewa, sun yi amfani da makamai masu guba.