Amurka: An bankado masu fasa-kwaurin sigari

'Yan sandan birnin New York na Amurka
Image caption Mahukunta a birnin New York na Amurka sun bankado wata kungiyar masu fasa-kwauri

Mahukunta a birnin New York na Amurka sun bankado wata kungiyar masu fasa-kwaurin taba sigari, sun kuma cafke mutane goma sha-biyar 'yan asalin Falasdinu.

A wani taron manema labarai na hadin gwiwa, Attoney Janar na New York da Kwamishinan 'yan sanda sun ce, mutanen sun sayar da tabar wadda ba a caji haraji kan ta ba ta darajar kudi dala miliyan hamsin da biyar an kuma yi fasa-kwaurin sigarin ne daga jihar Virginia.

A lokacin da 'yansanda suka cafke mutane biyu 'yan gida guda da suka yi amannar cewa sune jagororin kungiyar, sun gano zunzurutun kudi fiye da dala miliyan daya da rabi da akasari aka cunkusa a wasu ledojin shara.

Sun kuma yi amannar cewa 'ya'yan kungiyar da duka 'yan Palasdinu ne, na sayen taba sigarin ne daga jihar Virginia, inda ake da sassucin haraji, kana su sayar a birnin Newyork.

Ta hakan ne kuma sun zukewa biyan kudaden harajin da ya tasamma kimanin dala milliyan tamanin, tare da samun ribar dala miliyan goma.

Attoney Janar na New York da Kwamishinan 'yan sanda, Raymond Kelly sun ce sun matukar damu cewa, babu daya daga cikin kazamar ribar nan da aka gano a tsawo shekara guda da aka shafe ana bincike.

Sun kara da cewar irin wadannan kungiyoyin sun rika turawa kungiyoyin 'yan kishin Islama kamar na HizbuLLah da Hamas kudade.

Dukkanin mutanen goma sha biyar yanzu ana tsare da su, inda suke fuskantar tuhumar cin hanci da rashawa, halarta kudaden haram, da sauran laifuka.