An fara bukukuwan binne Chinua Achebe

Chinua Achebe
Image caption Chinua Achebe ya mutu yana da shekaru 82 a duniya

An fara bikin binne fitaccen marubucin nan dan Najeriya Chinua Achebe a mahaifarsa da ke garin Ogidi a Kudancin Najeriya.

Ana sa ran bikin na mako guda zai mayar da hankali wurin tunawa da abubuawan da marubucin yayi a tarihi.

Mr Achebe ya mutu a Amurka yana da shekaru 82 bayan wata gajeriyar rashin lafiya.

Daga cikin shagulgulan da za a yi a kwanaki bakwan sun hada da bikin marubuta da dandazon malaman jami'a da kuma bikin gargajiya, kafin a kai ga binne daya daga cikin garkuwan marubutan na Afrika.

Mahaifarsa ta Ogidi ita ce za ta kasance kan gaba wurin daukar nauyin bukukuwan.

Jana'izar addinin Kirista

Baki daga sassan duniya daban-daban ake sa ran za su halatta domin girmamawa ga mutumin da wasu da dama ke kira jagoran marubutan adabin zamani na Afrika.

A yayin da Mr Achebe ya kasance yana sukar 'yan siyasar Najeriya a fili, da dama daga cikinsu ne ake sa ran za su halarci bikin binne shin.

Za kuma a gabatar da bikin jana'iza na addinin Kirista da kuma al'adar kabilar Igbo.

Achebe ya yi fice ne wurin rubutun adabi - inda ya ke fito da al'adar kabilarsa ta Igbo.

Ya kuma yi rubuce-rubuce akan yanayin rayuwa a Afrika, da mulkin mallaka da kuma demokuradiyya da cin hanci.

A shekarar 1990 ne marubucin ya yi wani hadarin mota inda ya samu nakasa - abinda ya sa ya koma amfani da keken guragu.

Daga nan ne kuma ya koma Amurka da zama inda ya ci gaba da rubuce-rubuce da koyarwa a jami'ar har zuwa lokacin rasuwarsa.

Karin bayani