An dakatar da muhawara kan dokar kare mata a Afghanistan

Wasu mata a Afghanistan
Image caption Dokar ta hana cin zarafin mata da aurar da kananan yara

Wasu 'yan siyasa masu tsaurin ra'ayi a Afghanistan sun sa an dakatar da wata muhawara kan ko ya dace majalisar dokoki ta amince da wata doka dake hana cin zarafin mata.

Hayaniya ce ta barke a majalisar, kasa da minti sha biyar da wasu 'yan ra'ayin rikau suka nemi a soke dokar, wadda shugaba Hamid Karzai ya kafa ba tare da amincewa majalisar dokoki ba, shekaru hudu da suka wuce.

Wasu mata sun ce abin da ya farun ya sa musu shakku kan abubuwan da zasu faru bayan zabe na gaba, suna masu cewa akwai rashin tabbas kan ko shugaban Afghanistan na gaba, zai dauki wasu matakai na kare hakkin mata, musamman game da wannan doka.

A karkashin dokar, wadda ta haramta duka ko cin zarafin mata da kuma aurar da 'ya'ya matan da shekarunsu ba su kai ba, an daure daruruwan mutane, galibinsu maza.

Karin bayani