An kama wani jagoran dakarun sa kai a Ivory Coast

Shugaba Alassane Ouattara
Image caption Shugaba Alassane Ouattara

Hukumomi a Ivory Coast sun kama wani jagoran dakarun sa kai da ake zargi da hannu a daya daga cikin kisan kare-dangi mafi muni da aka aikata a tashin hankalin bayan zaben 2011.

Kungoyin kare hakkin jama'a sun ce mayakan Amade Oueremi sun bindige daruruwan magoya bayan tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo a garin Duekoue dake yammacin kasar.

Mutane kimanin dubu uku ne aka kashe a kasar ta Ivory Coast bayan da Mr Gbagbo ya kekasa kasa ya ki amincewa da nasarar abokin hamayyarsa, Alassane Ouattara a zaben shugaban kasar zagaye na biyu.

Yanzu haka dai Mr Gbagbo din na can yana zaman jiran shari'a a kotun hukunta laifukkan yaki ta duniya, ICC.

Karin bayani