An kashe wata babbar 'yar siyasar Pakistan

Zahra Hussein
Image caption Birnin Karachi ya yi kaurin suna wurin tashin hankali

An harbe har lahira wata babbar 'yar siyasar kasar Pakistan a birnin Karachi mai tashar jiragen ruwa na kudancin kasar.

Zahra Shahid Hussain ita ce babbar mataimakiyar shugaba ta jami'ayyar Pakistan's Movement for Justice party (PTI), wacce tsohon dan wasan Kuriket Imran Khan ke jagoranta.

Wasu 'yan bindiga ne akan babur suka kashe ta a wajen gidanta.

Kisan na ta ya zo ne a daidai lokacin da ake shirin sake wasu daga cikin zabukan da aka yi a karshen makon da ya gabata - wanda ake cece-kuce a kai.

Kawo yanzu babu tabbas kan dalilin kisan na ta.

Wakilin BBC Shahzeb Jillani a birnin Karachi ya ce Imran Khan ya zargi magoya bayan jam'iyyar MQM kan kisan, zargin da suka musanta.

Karin bayani