'Yan Boko Haram 'sun rasa na yi'

Sojojin Najeriya na sintiri
Image caption Sojojin Najeriya na sintiri

Rundunar sojan Najeriya ta ce a yayinda take ci gaba da kai farmaki a wasu yankuna na arewa maso gabashin kasar, mayakan kungiyar Boko Haram sun rasa na yi, kuma da dama daga cikinsu na tserewa ta kan iyakar kasar.

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, Hedkwatar tsaro ta Najeriyar ta ce daga jiya Asabar, an kashe wasu mayaka sha hudu na kungiyar ta Boko Haram, an kuma kama wasu ashirin, yayinda aka kashe sojojin gwamnatin uku a gumurzun.

Babu dai wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da labarin.

A halin da ake ciki kuma rahotanni na cewa sojoji sun hana motocin daukan kaya tashi daga Maiduguri zuwa garuruwan Baga da Kukawa da kuma Damasak inda ake kyautata zaton 'Yan Boko Haram sun kafa sansanoni kafin dakarun sojin Najeriya su fara kai hare- hare a yankunan.

Kan titin Baga dai na daga cikin unguwanni 12 na birnin Maidugurin da aka sanya dokar hana zurga-zurga ba dare ba rana a ranar Asabar.

Hakazalika wasu rahotannin na cewa fararen hula da dama na gudun hijira suna shiga makwabtan kasashen Kamaru da Nijar, domin kauce ma tashin hankalin.

Karin bayani