Jordan da Lebanon na bukatar agaji - Oxfam

Syria
Image caption Dubban 'yan Syria ne ke kwarara kasashen na Jordan da Lebanon

Kungiyar agaji ta Burtaniya Oxfam, ta ce kasashen Jordan da Lebanon na bukatar tallafin gaggawa domin su taimakawa dubban daruruwan 'yan gudun hijirar kasar Syria, wadanda suka kauracewa tashin hankalin da ake yi a kasarsu.

Oxfam ta ce karancin ruwan sha da rashin kyawun muhalli, gami da karuwar yanayin zafi, na mummunar barazana ga lafiyar 'yan gudun hijirar.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da 'yan Syria miliyan daya da rabi ne aka yiwa rijista a matsayin 'yan gudun hijira a Hukumance.

Kuma a cewar Oxfam, a zahiri take cewa mafiya yawansu ba za su koma gida a nan kusa ba, kuma masu masaukin bakinsu - kasashen Lebanon da Jordan na matukar bukatar taimakon kasashen duniya.

Ana cikin muwuyacin hali

Ta ce da dama daga cikin wadanda ke tsallaka iyaka domin neman mafaka, na zaune a matsugunan da basu dace ba, kamar shagunan da ba komai da wajen makabartu.

Lauren Wolfe, ta kungiyar kare hakkin mata ta Women Under Siege, ta sha kai ziyara sansanin Zaatari da ke Jordan.

Ta kuma shaida wa BBC cewa mutane na zaune cikin muwuyacin hali:

"Akwai matsalar kiwon lafiya a wurin. Na hadu da matan da ba sa iya shayar da jariransu, saboda iyayen ba sa samar da isassen nono," a cewarta.

A don haka kungiyar agajin ta Oxfam, ta nemi kasashen duniya da su tashi tsaye domin tun karar kalubalan da ake fuskanta na bukatar karin kudade.

Karin bayani