An yi jana'izar Zahra Shahid Hussain

Zahra Shahid Hussain
Image caption Daruruwan mutane ne suka halarci jana'izar Zahra Shahid

Daruruwan mutane ne suka halarci jana'izar mataimakiyar shugaban jam'iyyar PTI ta Pakistan, Zahra Shahid Hussain, wacce 'yan bindiga suka kashe a Karachi.

Wasu 'yan bindiga ne a kan babur suka harbe ta a wajen gidanta a birnin Karachi.

Jagoran jam'iyyar PTI Imran Khan ya dora alhakin kisan kan daya daga cikin abokan hamayyar siyasarsa.

A shafinsa na Twitter, Mr Khan ya ce ya dora laifin kisan kan shugaban jam'iyyar da ta fi rinjaye a Karachi MQM, Altaf Hussain - tuhumar da jam'iyyar ta MQM ta musanta.

Kisan ya zo ne a lokacin da ake sake zaben wasu mazabu a birnin na Karachi.

'Yan sanda na bincike kan ko kisan Mrs Hussain na da alaka da kokarin fashi da makami ko kuma siyasa ce.

Likitoci a asibitin Jinnah na birnin Karachi sun shaida wa BBC cewa binciken farko ya nuna cewa an harbe ta sau biyu a ka.

Sai a nan gaba ne za a fitar da cikakken sakamakon binciken.

Karin bayani