Nijar: Bankuna suna yajin aiki

Image caption Mahamdou Issoufou, shugaban Nijar

Yau harkokin banki sun tsaya cik a kusan dukkan faɗin Jamhuriyar Nijar, a sakamakon yajin aikin da ma'aikatan bankuna suka shiga.

Ma'aikatan suka ce, sun fara yajin aiki ne na kwanaki biyu, domin tilastawa gwamnati ta rage yawan harajin da ta ke cirewa daga albashinsu.

Wannan yajin aiki dai tuni ya soma shafar jama'a masu hulda da bankuna a kasar ta Nijar.