2014: Moses da Kalu sun ji rauni

moses
Image caption Victor Moses yana gurmuzu

Najeriya na fuskantar karancin 'yan wasan gaba, sakamakon raunin da Victor Moses da Kalu Uche suke fama da shi.

Wannan lamarin ya janyo Moses da Uche din ba za su bugawa Najeriya ba a wasanninta na neman gurbin zuwa gasar cin kofin kwallon duniya da kuma gasar zakarun nahiyoyi da za ayi a Brazil a wata mai zuwa.

Rauninsu cikas ne ga kocin Super Eagles, Stephen Keshi wanda a yanzu haka da dan wasansa Emmanuel Emenike ke fama da rauni.

Keshi yace" Abin takaici ne sun gaya mana cewar ba za su buga mana ba, kuma lokaci ya kuri mu gayyaci wasu, su maye gurbinsu".

Amma Keshi nada kwarin gwiwa a kan cewar Najeriyar za ta taka rawar gani a wasaninta da Kenya da kuma Namibia kafin ta garzaya birnin Rio don halartar gasar zakarun nahihoyin duniya.

Karin bayani