An rataye wasu 'yan Yemen biyar a Saudiyya

abdalla
Image caption Sarki Abdallah na Saudiyya

Hukumomin Saudi Arabia sun zartar da hukuncin kisa akan wasu 'yan kasar Yemen su biyar, da aka samu da laifin kafa wani gungun masu aikata fashi da makami.

Cikin wannan shekarar dai Saudi Arabi ta zartar da hukuncin kisa a kan mutane akalla arba'in da shida.

Su dai mutanen biyar 'yan asalin kasar Yemen an same su ne da laifin aikata fashi da makami da kuma lakadawa wani dan kasar ta Saudiyya duka har sai da ya mutu.

Bayan dai an zartar da hukuncin kisa akan mutanen biyar a garin Jizan dake kudu maso yammacin Saudiyya, an rataye gawarsu a baiyanar jama'a.

Aikata laifuka kamar fashi da makami na karuwa a kasar ta Saudiyya, kuma hakan yana yin barazana ga sha'anin tsaron 'yan kasar.

Karin bayani