Guguwa ta hallaka mutane 25 a Amurka

okhaloma
Image caption Gidaje da dama sun lalace a Oklahoma

Wata mahaukaciyar guguwa ta ratsa ta ta wani yanki dake wajen birnin Oklahoma a Amurka, inda ta shafe anguwannin yankin.

An tabbatar da mutuwar mutane akalla ashirin da biyar cikinsu hadda kananan yara wadanda makaranttarsu ta yi kaca-kaca.

Masu aikin ceto na ta kokarin gano wadanda ke da rai, suna kasa kunne su ji muryar wadanda suka makale a cikin baraguzai.

Mahukaciyar guguwar da ta afkawa yankin na da karfin gaske, inda ta yi raga raga da gine gine da karafa da katakwaye.

Shugaba Obama ya bayyana lamarin a matsayin wanda ya yi munin gaske ya kuma yi alkawrin twallafi daga gwamnati.

Ko a shekara ta 1999, dubban gidaje ne suka rushe lokacin da irin wannan guguwar da ba a taba ganin irinta ba a tarihi ta afkawa yankin.

Karin bayani