An kusa kammala aikin ceto a Amurka

Image caption Mahaukaciyar guguwar ta lalata sassa da dama na Oklahoma

Ma'aikatan ceto a Amurka sun ce suna dab da kammala binciken mutanen da suka rage da rai bayan mahaukaciyar guguwar da ta yi kaca-kaca da birnin Oklahoma.

Mutane akalla ashirin da hudu ne suka mutu yayin da wasu fiye da dari biyu suka samu raunuka sanadiyar aukuwar guguwar.

Tara daga cikin wadanda suka mutu kananan yara ne.

Babban jam'i'in ma'aikatan kwana-kwana, Gary Bird, ya ce yana da tabbacin cewa babu sauran wasu gawarwaki ko masu rai da za a samu a baraguzan gine-ginen gidaje da makarantu da shagunan da guguwar ta rugurguza.

Gwamnar Oklahama, Mary Fallin, ta ce mahukunta na fama wajen gano adadin yankunan da mahaukaciyar guguwar ta yi wa barna, tana mai cewa jihar za ta murmure daga wannan masifa.

Ta ce: ''Jihar [Oklahoma] tana cikin wani lokaci na jarraba. Lokaci ne na jimami, saboda mun fuskanci daya daga cikin munanan guguwa da bala'i da ba mu taba fuskanta ba. Amma duk da halin da muke ciki na masifa da rasa rayuka mun jajirce; kuma da taimakon jama'armu za mu yi nasara. Za mu sake gina jiharmu''.

Karin bayani