Doka game da bakin-haure ta samu karbuwa a Amurka

Image caption Shugaba Obama ya yi marhabin da matakin

Wani kudirin doka da zai bai wa miliyoyin bakin-haure damar samun takardun shaidar zama 'yan kasa a Amurka ya samu karbuwa kuma za a tafka muhawara a kansa a majalisar dattawan kasar.

Sabuwar dokar za ta ba bakin-haure miliyan goma sha daya da ke zaune Amurka ba tare da izini ba damar samun kwarya-kwaryan matsayi na bakin da aka san da zamansu.

Bayan sun shafe shekaru goma za su iya sayen kati na shaidar zama dan kasa na dindindin.

'Yan jam'iyyar Republican da ke kwamitin da ke kula da harkokin shari'a sun sassauta ka'idoji a kan kwararrun ma'aikata 'yan kasashen waje.

A nasu bangaren, 'yan Democrat sun yi watsi da shirin kyale Amurkawa su rinka daukar nauyin ma'aurata masu jinsi daya da za a bai wa takardun zaman kasar na dindindin.

Shugaba Obama ya yi marhabin da matsayin da majalisar ta dauka, yana mai cewa koda yake an yi wa dokar gyare-gyare, har yanzu tana kunshe da burinsa na kawo sauyi ga dokokin shige da ficen Amurka.

Karin bayani