'Tayin afuwa ne ya janyo karin hare-hare a Najeriya'

moro
Image caption Ministan harkokin cikin gida a Najeriya, Abba Moro

Ministan harkokin cikin gidan Najeriya, Mista Abba Moro ya shaidawa BBC cewa, tayin afuwar da gwamnati ta yiwa 'yan kungiyar Boko Haram, shi ne ya kara zafafa fadan da ake yi da su.

Ministan yace, masu tsananin ra'ayi daga cikin 'yan kungiyar ta Boko Haram, sun tsananta hare-haren ne, domin su nuna irin karfin da suke da shi, bayan sun yi watsi da tayin ahuwar da aka yi musu.

Mista Moro yace " Lokacin da gwamnatin tarayya ta ayyana wani tsari na yin afuwa, kuma ta kafa kwamiti da zai duba yiwuwar tattaunawa da 'yan kungiyar Boko Haram, kwatsam sai wasu masu kaifin kishi daga cikin 'yan kungiyar suka yi fatali da kokarin gwamnatin, kuma don su nuna cewar suna da karfi, sai suka tsananta kai hare-hare, a kan gine-ginen gwamnatin da cibiyoyin hada-hada".

A iya cewa dakarun Najeriya na yaaki na cikin gida mafi girma tun bayan yaakin basasa ko kuma yaakin Biafara da aka yi tsakanin gwamnati da kuma 'yan kabilar Ibo a cikin shekarun 1960.

A halin yanzu kuma dai sojojin kasar na kokarin fatattakar 'yan Boko Haram din wadanda suka yi karfi sosai a jihohin arewa maso gabashin kasar musamman Borno da Yobe.

Karin bayani