Shugabannin Turai sun bukaci daukar mataki kan kin biyan haraji

Tutar kungiyar Tarayyar Turai
Image caption Tutar kungiyar Tarayyar Turai

Austria ta shiga sahun wasu kasashen kungiyar tarayyar Turai wajen yin kiran a dauki matakai a kan masu kaucewa biyan haraji, duk da cewa, tsarin bankunan kasar ta Austria yana cike da sirri.

Shugaban gwamnatin Austria ya ce, kamata ya yi Turai ta dauki matakan da suka zarta musayar bayanan ajiya a bankuna, domin yaki da matsalar kaucewa biyan haraji:

Shugabannin kasashen Turai dai suna tattaunawa a kan matakan da za su dauka domin dakile matsalar kaucewa biyan haraji musamman daga bangaren manyan kamfanoni da kuma hamshakan attajirai.

An dai yi kiyasin cewa, kasashen Turai suna yin asarar makuden kudade sakamakon kaucewa biyan haraji.

Karin bayani