'Yan ta'adda sun kashe soja a London

woolwich
Image caption 'Yan sanda sun rufe titin zuwa Woolwich dake kudu maso gabashin London

Gwamnatin Birtaniya ta yi zargin cewa, harin ta'addanci ne aka kaiwa wani mutum a nan London, inda aka hallaka shi.

Shaidu suka ce, wasu mutane ne biyu, suka yi ta daba wa mutumen wuka har sai da ya mutu.

Ana jin mutumen soja ne, daga baya 'yan sanda sun harbi maharan, wadanda a yanzu suke can kwance a asibiti.

Praministan Birtaniyar, David Cameron, yayi Allah wadai da abinda ya kira " mummunan kisa".

Mista Cameron ya katse ziyarar da yake yi a Faransa domin komowa gida, inda zai shugabanci taron kwamitin gaggawa na COBRA.

Karin bayani