Cameron zai jagoranci taro kan tsaron Burtaniya

Image caption Mista Cameron ya ce za su sanya kafar wando daya da 'yan ta'adda

Firayim Ministan Burtaniya, David Cameron, zai jagoranci taron gaggawa da kwamatin kula da rikice-rikice zai gudanar ranar Alhamis, bayan kisan gillar da aka yi wa wani mutum a kusa da barikin soji na birnin London a ranar Laraba.

Mutane biyu da ke wasu kalamai masu alaka da addinin musulinci ne dai aka ce sun kashe mutumin da ake kyautata zaton soja ne, ta hanyar amfani da wuka da kuma wani abin datsa kashi a Woollwich.

Mista Cameron ya katse ziyarar da yake yi a Faransa inda ya koma gida Burtaniya saboda aukuwar lamarin da mahukunta suka bayyana da cewa harin ta'addanci ne.

Mutane da dama ne dai suka tur da aukuwar wannan lamari, cikinsu har da al'umar musulmi da ke Burtaniya.

Shugaban kungiyar the Ramadhan Foundation, Mohammed Shafiq, ya ce harin da aka kai ba shi da alaka da musulinci.

A cewarsa, ''Wadannan mutane[ da suka yi kisa] na ganin cewa za su iya yin amfani da tashin hankali wajen gallazawa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba. Suna ganin cewa saboda abubuwan[ tashin hankali] da ke faruwa a Afghanistan and Iraq da ma wasu sassan duniya, hakan ya halasta kai wa 'yan uwansu 'yan Burtaniya hari. A gaskiya, hakan ya sabawa addinin musulinci''.

Wani babban jami'an 'yan sandan Woolich, Duncan Slade, ya shaidawa BBC cewa an tsaurara matakan tsaro a kudu maso gabashin birnin London, kuma suna gudanar da binciken ababen hawa.

Karin bayani