Amurka za ta dakatar da jirage marasa matuka idan... — Obama

Image caption Shugaba Obama ya ce za a rika amfani da jiragen marasa matuka ne kawai idan aka tabbatar Amurkawa na fuskantar barazana.

Shugaba Obama na Amurka ya ce ya tsara wasu sababbin ka'idoji na amfani da jiragen sama marasa matuka wajen kai hari a kan kungiyoyin 'yan ta'adda.

Kodayake bai yi cikakken bayani game da batun ba, amma Mista Obama ya jaddada cewa ya kamata a yi amfani da jiragen ne kawai idan Amurkawa na fuskantar matukar barazana daga 'yan ta'adda ko kuma idan aka tabbatar cewa harin da za a kai ba zai shafi fararen hula ba.

A cewarsa, ''Wannan sabuwar fasaha [ ta amfani da jiragen sama marasa matuka] ta dora alamar tambaya dangane da ko wa za a kai wa hari, da kuma dalilin yin hakan; da farar hular da harin zai shafa, da kuma hatsarin da hakan ke da shi na kirkiro mana sababbin makiya, da ma ko shin wannan mataki ya dace a dokokin Amurka da na kasashen duniya''.

Mista Obama ya jaddada matsayinsa na rufe sansanin gwale-gwale na Guantanamo Bay da ke Cuba.

Ya ce za a rika tura firsunonin da ake tsare da su a Guantanamo Bay din zuwa Yemen, sannan ya bai wa ma'aikatar tsaron Amurka umarni ta gurfanar da wasu a kotun soji da ke Amurka.

Karin bayani