Kungiyar kasashen Afirka ta cika shekaru 50

Image caption Shugabannin kasashen Afirka sun kafa kungiyar shekaru hamsin da suka wuce

Shugabannin kasashen Afrika sun hallara a birnin Addis Ababa domin bikin cika shekaru hamsin da kafa kungiyar hada kan Afirka wadda ta zamo kungiyar Tarayyar Afrika AU.

A shekarar 1963 ne shugabannin nahiyar suka gana a babban birnin kasar ta Habasha inda suka kafa kungiyar hada kan kasashen Afrika OAU.

A karkashin kungiyar ne kasashen ke tattaunawa kan batutuwan da suka shafi tsaro da manufofin tattalin arziki da hulda da kasashen waje.

An dai shafe rabin karni kungiyar ba ta cimma wannan buri ba, to amma a ranar Asabar za a gudanar da shagulgula, da kuma yin muhawara kan batutuwan da suka shafi kishin nahiyar Afirka, da kuma farfado da ita daga mawuyacin halin da take ciki.

Mahalarta taron na cike da kwarin gwiwa, watakila saboda yadda tattalin arzikin nahiyar ke bunkasa, da kuma yadda akalla kasashen da suka fada cikin yaki - irinsu Rwanda, Sierra Leone, har ma da Somalia a yanzu suke murmurewa.

Karin bayani