Ana bukukuwan cika shekaru hamsin da kafa kungiyar kasashen Afrika

zauren taron Tarayyr Afrika
Image caption zauren taron Tarayyr Afrika

Shugabanni daga kasashen Afrika daban daban na ci gaba da bukukuwan cika shekaru hamsin da kafa kungiyar hada kan kasashen Afrika, wadda a yanzu ta koma tarayyar Afrika.

Lokacin bude bikin a birnin Addis Ababa, Praministan Ethiopia, Hailemariam Desalegn, ya ce nauyin dake wuyan tarayyar Afrika a yau da kuma a nan gaba shi ne gina wata al'umma mai matsakaicin karfin tattalin arziki a nahiyar, domin fitar da ita daga kangin talauci.

Wani wakilin BBC a birnin ya ce irin habakar tattalin arzikin da aka samu a Afrika a baya baya nan, ko kusa ba yana nuna cewa an kusa cinma wannan mafarki na ganin daukacin al'umar nahiyar ta Afrika sun kasance masu matsakaicin abin hannu ba.