Makaman roka sun dira a birnin Beirut

Makaman roka sun dira a Kudancin Lebanon
Image caption Akalla mutane hudu ne suka jikkata a harin

An harba wasu makaman roka biyu a wani yanki na Kudancin Lebanon wanda ke karkashin ikon kungiyar Hezbollah - inda mutane da dama suka samu raunuka.

Rahotanni sun ce wasu daga cikin wadanda suka samu raunukaN ma'aikata ne 'yan kasar Syria.

Daya daga cikin makaman ya fada ne a wani wurin sayar da motoci, inda ya lalata motoci da dama.

Yayin da daya kuma ya fada kan wani gida.

Ministan cikin gida na kasar ta Lebanon ya ziyarci wurin domin ganewa idanunsa abinda ya faru.

Wannan lamari dai na zuwa ne sa'o'i kadan bayan jawabin da jagoran Hezboullah Hassan Nasrullah ya yi, inda ya sha alwashin samun nasara tare da gwamnatin Syria a rikicin da take yi da 'yan tawaye.

"Wannan yaki kamar sauran yake-yaken da suka gabata, mu ne akan gaba! Mu ne za mu samu nasara, idan Allah ya yarda," a cewarsa.

Kungiyar Hezbolla na marawa dakarun gwamnatin Syria baya a yakin da ake a yankin Qusair da ke iyaka da kasar Lebanon.

Karin bayani