Rikicin Syria ya shafi Lebanon! Inji Nasrullah

Mayakan Hezbollah
Image caption Mayakan Hezbollah

Jagoran kungiyar Hebullah ta Lebanon ya ce mayaknsa zasu ci gaba da kasancewa a cikin rikicin kasar Syria har sai zuwa karshen lamarin, domin kuwa akwai bukatun kasar Lebanon.

A wani jawabi da aka watsa ta talabijin, Hassan Nasrallah ya ce idan 'yan tawayen 'yan Sunni suka kwace iko da kasar Syria makwabciyarsu, zasu kasance barazana ga daukacin al'umar Lebanon-- 'yan shi'a, da 'yan Sunni da ma kiristoci.

Ya ce kungiyarsa ba za ta taba amintaka da 'yan tawayen Syria ba wadanda a cewarsa Amurka da Isra'ila ke tallafawa.

Karin bayani