Musulmai a Landan na cikin fargaba

Wata kungiya dake kokarin hada kan mabiya addinai daban daban a Birtaniya, na cewa Musulmai na zaman fargaba tun bayan da wasu masu da'awar kishin Musulunci suka kashe wani sojan Birtaniya a kan wani titin birnin London.

Kungiyar mai suna Faith Matters, ta ce an samu karuwar yin cin fuska ga musulmai tun bayan da aka daddatsa wannan soja ranar Laraba.

Ta ce an samu koke sama da dari da sittin da biyu na cin fuska ga musulmai cikin kwanaki biyu, wadanda suka hada da kai hare hare a masallatai da kuma kunduma ashariya.

Shugabanin Musulmi sun fito sun yi Alah wadai da kashe wannan soja.