Fadan kwace Qusair ya yi zafi

Garin Qusair
Image caption Fada kan garin Qusair

Bangarorin dake fada da juna a rikicin kasar Syria na cewa sabon fada ya barke a garin Qusayr dake yammacin kasar.

Kafar yada labaran gwamnati na cewa dakarun gwamnatin sun tasamma garin ne ta bangarori uku, inda suka kashe 'yan tawaye masu yawa.

Masu fafutuka sun ce an yi ta luguden bamabamai a wasu yankunan birnin dake hannu 'yan tawaye, haka nan kuma mayakan kungiyar 'yan Shia ta Lebanon, Hizbullah dake mara baya ga gwamnatin Syria na kai masu hare hare.

George Sabra shi ke rikon shugabancin kawancen kungiyoyin 'yan tawaye, ya kuma soki Hizbullah kan shiga fadan.

Inda ya ce, wannan ta'addanci ne da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin duniya.

Hakan na faruwa ne a gaban idanun duniya, kuma kowa na kallo.

Tun ranar Lahadi fadan kwace iko da Qusayr din ya barke.

Karin bayani