An taba kama Michael Adebolajo a Kenya

masu ajiye furanni a inda aka kashe sojan Birtaniya
Image caption masu ajiye furanni a inda aka kashe sojan Birtaniya

Hukumomi a Birtaniya sun tabbatar da cewa wani dan Birtaniya, daya daga cikin mutane biyun da ake zargi da daddatsa wani soja har ya mutu a kan wani titi na birnin London, an taba kama shi a Kenya , shekaru biyu da suka wuce.

Ofishin harkokin wajen Birtaniya ya ce ya taimaka ma Michael Adebolajo da shawarwari.

Shugaban sashen yaki da ayyukan ta'adanci na gwamnatin Kenya, Boniface Mwaniki ya shaidawa kampanin dillancin labaru na AP cewa an kama Mr Adebolajo ne a watan Nuwamban 2010 bisa zargin cewa yana shirin shiga yaki a bangaren mayakan kishin Islama a Somalia.

A yanzu mutane shidda ne 'yan sanda ke tsare da su game da kisan sona na Birtaniya ranar Laraba.

Karin bayani