Mutane akalla sittin da biyar sun mutu a wasu hare-hare a Iraki

Hare-hare a Iraki
Image caption Hare-hare a Iraki

Wasu hare haran bama-baman mota a ciki da kewayen Bagadaza, babban birnin Iraqi , sun hallaka mutane akalla sittin da biyar.

Jami'an 'yan sanda sun ce mutane da dama sun ji raunuka a hare haren, wadanda aka kai a kasuwannin dake cike da jama'a a wasu anguwanni na galibi 'yan Shi'a.

Zein Al-Abidin ya ga abin da ya faru, kuma bayan ya nuna takaicinsa ya nemi sanin ko wane laifi wadannan mutane da aka kai ma harin suka yi da aka kashe su?

Ya ce ya ji mamakin yadda za a halaka kananan yara 'yan shekaru hudu da ba basu ji ba ba su gani ba .

Babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai hare haren.

Wannan dai na zuwa ne yayinda ake kara samun zaman dar dar na siyasa tsakanin mabiya Shi'a masu rinjaye, dake rike da mulki, da kuma 'yan Sunni.