Barazanar ta-da kayar baya a Afrika

'Yan Boko Haram
Image caption Matasa masu zaman kashe wando na sha'awar shiga kungiyoyin addini masu dauke da makamai

Titin Sardauna Cresent, wanda ke kusa da filin wasa na Ahmadu Bello a birnin Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya, babban titi ne wanda ke da yawan hada-hada.

Sai dai kuma a bara wata mota makare da ababen fashewa ta fashe a titin, al'amarin da ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane da dama, da lalata gidajen da ke kusa da titin da kuma ababen hawa.

Jami'an tsaro dai sun dora alhakin wannan fashewar a kan masu tayar da kayar baya.

Abin tambaya a nan shi ne: menene yake sanya wadannan mutane aikata hakan? Kuma menene yake ingiza matasa cikin wadannan mutane?

Wani matashi wanda ya ce ba ya so a fadi sunan sa ya shaidawa BBC cewa, tun bayan kammala karatunsa shekaru bakwai da suka gabata yake neman aiki, kuma babu abin da gwamnati ke yi a kan haka.

A cewar matashin, "Ina ganin 'yan siyasa suna hawa motoci masu tsada, suna kai 'ya'yansu karatu kasashen waje, ina jin ba dadi; hakan ya sa wani lokaci sai na ji kamar na shiga aikata abin da bai dace ba.

"Sai dai kuma idan na tuna da addinina, sai na bar komai ga Allah na kuma ci gaba da addu'a a kan Allah ya bani aiki mai amfani".

A kwanannan ne gwamnatin Najeriya ta bukaci sulhu da masu tayar da kayar bayan—tayin da tuni suka yi watsi da shi.

Shi dai matashin da ya zanta da BBC yana jin cewa karshe ma tayin afuwar ba zai kai ga samun abin da ake bukata ba; a maimakon haka sai ma ya sa daukar bindiga ya zama abin sha'awa a wajen matasa.

Matashin ya ci gaba da cewa, "Ko ni na kan ji kamar na shiga cikin kungiyar Boko Haram, mai yiwuwa na yi sa'a a yi min tayin afuwa. Ka ga ni ma sai na samu abin da mayakan sa kai na yankin Neja Delta ke samu bayan an yi musu afuwa".

Wannan wani matashi ke nan mai shekaru talatin da biyu da haihuwa—matasa ire-irensa suna nan da yawa; dubun dubatarsu masu zaman kashe wando suna ta gararamba a titi, cike da haushin komai da kowa.

Wani abu kuma da ke ingiza matasa daukar makamai shi ne rashin cikakken ilimin addini, kamar yadda Shaikh Dokta Ahmad Abubakar Mahmud Gummi, wani malamin addinin Islama a Kaduna, ya bayyana.

Image caption Jami'an tsaron Najeriya sun ce sun dai-daita maboyar masu tayar da kayar baya a gandun dajin Sambisa da ke jihar Borno

"Musulunci ya haramta kashe rai, ko Musulmi ko wanda ba Musulmi ba, kuma duk wanda ya yi niyyar kashe wani ko kuma kashe kansa, to juya masa kwakwalwa aka yi".

Haka zalika wani masanin halayyar rayuwar dan-Adam, wanda ya assasa wata kungiya mai zaman kanta a Kaduna mai suna Gidauniyar Triumphant Youth, Ibrahim Yusif Gombe, ya yi amanna cewa: "Talauci na cikin abubuwan da ke haddasa wadannan abubuwa. Dalilina na fadar hakan shi ne, a arewacin kasarmu ta Najeriya za ka ga matasa masu hazaka suna zaman kashe wando babu aikin fari balle na baki—idan garin ya yi musu zafi su kan shiga shaye-shaye domin su samu saukin bakin cikin da suke ciki.

"Kuma ko me aka sanya su su aikata idan dai har za su samu kudi suna yi. Wannan kuma laifin shugabanni ne tun da ba sa abin da ya kamata su yi".

Fargabar da kasashen Yamma ke nunawa dangane da tsattsauran ra'ayin addinin Musulunci a Najeriya ya rataya ne a kan tunanin cewa akwai alaka tsakanin masu tsattsauran ra'ayin na Najeriya da kungiyar Al-Ka'ida a yankin Maghreb, da ma na Mali.

Ana ta muhawara a kan wannan alaka, ko da yake har yanzu babu wata kwakkwarar hujjar da ke nuna cewa akwai ta.

Abin da ya fito fili dai shi ne cewa matsalolin cikin gida ne suka ingiza matasa da dama a arewacin Najeriya su shiga kungiyoyin Musulunci masu dauke da makamai.

Karin bayani