Najeriya: PDP ta dakatar da Amaechi

Tambarin jam'iyyar PDP
Image caption Jam'iyyar PDP mai mulki a Najeriya ta dakatar da Gwamna Chibuike Rotimi Amaechi na Jihar Rivers

Jam'iyyar PDP mai mulki a Najeriya ta bayar da sanarwar dakatar da Gwamna Chibuike Rotimi Amaechi na Jihar Rivers daga jam'iyyar.

A wata sanarwa da ta fitar mai dauke da sa-hannun Sakataren Yada Labaranta na kasa, Olisa Metuh, jam'iyyar ta ce ta dakatar da gwaman ne bayan wani taro da Kwamitin Gudanarwarta na kasa ya yi.

"Kwamitin Gunarwa na Kasa", a cewar sanarwar, "yayin wani taron gaggawa da ya gudanar ranar Litinin 27 ga watan Mayu, 2013, ya duba koken da Kwamitin Zartarwa na PDP a Jihar Rivers ya gabatar yana kalubalantar Chibuike Rotimi Amaechi, Gwamnan Jihar Rivers, saboda ya saba Sashe na 58 karamin Sashe na 1(b), da (c), da (h), da kuma (m) na Kundin Tsarin Mulkin Jam'iyyar PDP ta hanyar bijire wa umarnin Kwamitin Zartarwar Jihar Rivers a kan ya sake shawara dangane da rusa zababben Kwamitin Zartarwa na Karamar Hukumar Obiokpor...".

Cif Metuh ya kara da cewa Kwamitin Gudanarwar jam'iyyar ta PDP ya yi amfani da ikon da Kundin Tsarin Mulkin jam'iyyar ta ba shi ya dakatar da gwamnan, sannan kuma ya mika batun ga kwamitin ladabtarwa na jam'iyyar don ya dauki mataki na gaba.

Idan ba a manta ba, a karshen makon jiya ne gwamnonin kasar suka sake zaben Mista Amaechi a matsayin shugaban Kungiyar Gwamnoni ta Najeriya, bayan wata zazzafar takara.

Rahotanni dai sun nuna cewa Gwamna Amaechi ba ya samun goyon bayan Fadar Shugaban Kasa da ma jam'iyyar tasu ta PDP.

Karin bayani