Sergeant Bales ya amince zai amsa laifin kisan kai

Staff Sergeant Robert Bales na Amurka
Image caption An zargi Robert Bales da kashe mata da yara a Afghanistan

Sojan nan na Amurka da aka yi zargin ya kashe wasu 'yan Afghanistan farar hula goma sha-shida a bara ya amince zai amsa laifinsa ga tuhumar da aka yi masa ta aikata kisan kai.

Lauyan na Sergent Robert Bales ya ce zai nemi afuwa tare da amsa laifinsa don kaucewa hukuncin kisan kai.

Masu gabatar da kara sun ce Sergent Bales ya fita daga sansaninsa ne dake kudancin Afghanistan wata rana da sanyin safiya, inda ya je ya kai hari a wasu Kauyuka biyu dake kusa da sansanin, inda ya kashe akasarin Mata da Kanana Yara.

Kashe-kashen dai nan sun haddasa mummunan bore wanda ya sa Amurka ta dakatar da tura sojoji su kai hari a kasar ta Afghanistan ala tilas.

Karin bayani