Ana tuhumar kamfanin intanet da yin zamba-cikin-aminci

Jami'an gwamnatin Amurka sun ce wannan mataki hanya ce ta  kawar da damfara ta intanet
Bayanan hoto,

Jami'an gwamnatin Amurka sun ce wannan mataki hanya ce ta kawar da damfara ta intanet

Masu shigar da kara a Amurka sun tuhumi kamfanin musayar kudi ta kwamputa mafi girma a duniya da yin amfani da intanet wajen yin sama-da-fadin makudan kudade.

Ofishin babban mai shigar da kara na Amurka ya ce kamfanin da ke Costa Rica, Liverty Reserve, ya yi safarar kudaden da suka kai dala biliyan shida ta haramtacciyar hanya.

Masu shigar da karar sun siffanta kamfanin — wanda a yanzu aka dakatar da shi— a matsayin wani babban mai aikata laifi a boye.

Sun ce manyan masu aikata laifuka na amfani da bankin a matsayin babbar hanyar da suke amfani da ita wajen hada-hadar kudaden da suke samu daga safarar miyagun kwayoyi, da fina-finan batsa na kananan yara, da kuma satar bayanan al'uma.